Chelsea ta doke Barcelona a wasan sada zumunci a Japan

Tammy Abraham Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Abraham ya ci kwallon ne bayan tun farko ya zubar da wata kyakkyawar dama

Kwallon da Tammy Abraham da Ross Barkley suka zura ta bai wa Chelsea damar doke Barcelona 2-1 a wasan sada zumunci a Japan.

Abraham ne ya fara zura kwallon bayan da ya yanke gola kafin Barkley ya zura ta biyu.

Ivan Rakitic ne ya zura kwallo dayan da Barcelona ta samu a wasan.

A wasan ne kuma dan wasan da Barca ta sayo kan fam miliyan 107 Antoine Griezmann ya fara buga wasansa na farko.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Christian Pulisic ya koma Chelsea daga Borussia Dortmund a watan Janairu
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Griezmann ya buga wasansa na farko a Barcelona

Labarai masu alaka

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba