Kasuwar musayar 'yan kwallo: Lokaci na kurewa Man Utd da Arsenal

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Paris St-Germain ta shiga gaban Juventus a yunkurin sayen dan kwallon Tottenham Danny Rose kuma suna fatan kammala cinikin kan fan miliyan 20, in ji jaridar (Sun).

ShugabanTottenham Daniel Levy na son daga farashin dan wasan baya Toby Alderweireld zuwa fam miliyan 40 idan har babu wanda ya sayi dan wasan a kan fam miliyan 25 nan da ranar Juma'a kamar yadda kwantiraginsa ta tanada, a cewar (Telegraph).

Shugaban kulob dinManchester United Ed Woodward ba zai bi kungiyar zuwa atisayen da take yi ba domin kammala cinikayyar wasu 'yan wasa kafin a rufe kasuwar musayar 'yan kwallo, in ji (ESPN).

Woodward na da kwarin gwiwar kammala cinikin dan wasan baya na Leicester Harry Maguire, da na matashin dan wasan tsakiya na Newcastle Sean Longstaff, in ji (London Evening Standard).

Nan da makonni biyu masu zuwa ne kocinArsenal Unai Emery zai yanke shawarar ko zai saki matashin dan wasan Ingila Reiss Nelson, zuwa Hertha Berlin a matsayin aro ko kuma a'a, a cewar (Sun).

Arsenal na kuma fatan ganin ta sayi Wilfred Zaha daga Crystal Palace kafin a rufe kasuwar musayar 'yan kwallon.

Har yanzu kocinLiverpool Jurgen Klopp na son sayen dan wasa guda kafin a rufe ksuwa, amma ya bayyana cewa kulob ba zai kashe kudi kamar bara ba, inda suka kashe fam miliyan 170, in ji (Liverpool Echo)

Labarai masu alaka

Karin bayani