La Liga za ta iya soke tafiyar Griezmann Barcelona

Antoine Griezmann Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Da ma dai an yi hasashen Antoine Griezmann zai koma Barcelona tun kafin farashinsa ya yi kasa

Shugaban gasar kwallon kafa ta La Liga Javier Tebas, ya bayyana cewa za a iya dakatar da komawar Antoine Griezmann zuwa Barcelona saboda takaddama kan farashin dan wasan.

Kungiyar Atletico Madrid da koka bayan da Barcelona ta sanar da daukar dan wasan na Faransa kan Yuro miliyan 120 kimanin fam miliyan 107 a ranar 12 ga watan Yuli.

Farashin dan wasan ya sauko daga Yuro miliyan 200 zuwa 120 a ranar 1 ga watan Yuli, sai dai Atletico ta bayyana cewa an yi yarjejeniyar ce kafin wannan rana.

''Zai iya yiwuwa a dakatar da sayen dan wasa,'' in ji Mista Tebas.

''Gasar La Liga za ta yanke hukunci kan matakin da za ta dauka na gaba.''

Tuni dai Griezmann ya buga wasa a sabon kulob din nasa inda Chelsea ta lallasa kulob dinsa 2-1 a Japan.

Tebas ya bayyana cewa: Kungiyar Atletico ta bayar da takardar koke inda take shakku kan bayar da lasisin Griezmann zuwa Barcelona.

A Disambar 2007 ne Atletico din ta kai karar Barcelona zuwa ga hukumar FIFA inda ta yi zargin cewa Barcelona suna neman Griezmann ta hanyar da ta sabawa doka.

A kakar kwallon da ta gabata ne dai dan kwallon ya ki amincewa da neman da Barcelona ta yi masa, amma Atletico ta yi zargin cewa Barcelona ta tattauna da shi a watan Maris, inda ta zarge ta da yi mata cin fuska.

Labarai masu alaka