Marco Asensio zai yi jinyar guiwa ta wata tara

Marco Asensio Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption An yi waje da Marco Asensio a minti na 64 bayan da ya ji rauni a karawar ta Kofin International Champions

Dan wasan gaba na gefe na Real Madrid Marco Asensio ba zai samu damar buga yawancin wasannin kakar 2019-20 ba, bayan da ya ji rauni a guiwarsa a karawarsu da Arsenal ranar Laraba.

Asensio, mai shekara 23, ya daga ragar Arsenal a wasan a Amurka, amma daga baya aka yi waje da shi bayan da ya ji raunin.

A wata sanarwa da Real Madrid ta fitar, ta ce, "An bincika an gano cewa dan wasan ya ji rauni ne a guiwarsa ta kafar hagu.

"Kuma za a yi wa dan wasan tiyata a 'yan kwanakin da ke tafe."

Arsenal na gaba a wasan da ci 2-0 daga kwallayen da Alexandre Lacazette da Pierre-Emerick Aubameyang suka ci musu.

Sai dan wasan na tawagar Sifaniya, Asensio ya farke wa Real a minti na 59, bayan da aka sako shi a kashi na biyu na wasan, bayan tun da farko Gareth Bale ya ci daya.

Sai dai kuma minti biyar bayan ya farke ne ya ji raunin a gasar ta cin Kofin International Champions Cup, wanda Real ta yi nasara a bugun fanareti da ci 3-2.

Rahotanni daga Sifaniya na cewa kila dan wasan zai yi jinya har ta tsawon wata tara, wanda hakan zai sa da wuya ya samu buga gasar cin kofin kasashen Turai ta Euro 2020, idan kasarsa ta samu tikitin tafiya.

Raunin zai iya kuma tasiri a kan burin Arsenal na karbar aron dan wasan tsakiya na Real Madrid din Dani Ceballos, mai shekara 22.

Bayan wasan kociyan Arsenal Unai Emery ya ce raunin na Asensio zai iya kasancewa labari maras dadi a wurinsu, kuma ba shi da tabbacin ko Real Madrid za ta yarda ta bayar da aron Ceballos yanzu.

Labarai masu alaka

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba