Man U na son Eriksen, Arsenal ko Everton - ina Zaha zai tafi?

Christian Eriksen Hakkin mallakar hoto NurPhoto
Image caption Saura shekara daya kwantiragin Christian Eriksen ta kare a Tottenham

Kungiyar Tottenham ta tuntubi Juventus domin ta sayar mata da dan wasan gaba dan tawagar Ajentina Paulo Dybala, mai shekara 25, wanda aka yi masa kudi fam miliyan 80, in ji (Evening Standard)

Paris St-Germain ta amince ta sayi dan wasan tawagar Senegal daga kungiyar Everton Idrissa Gueye, mai shekara 29, a kan fam miliyan 28, kamar yadda jaridar (Mail) ta ruwaito.

Haka kuma Everton din za ta kara tattaunawa da Crystal Palace, a wannan makon domin sayen dan wasan tawagar Ivory Coast Wilfried Zaha, mai shekara 26, a kan fam miliyan 80, in ji (Sky Sports)

Kociyan Liverpool Jurgen Klopp ya kawar da yuwuwar sake dawo da tsohon dan wasansu, dan Barcelona da Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 27, wanda ya bar Anfield a kan fam miliyan 142 a 2018, in ji (ESPN)

Manchester United kuwa ta bukaci a ba ta bayani a kan makomar dan wasan tsakiya na Tottenham Christian Eriksen, mai shekara 27. Dan wasan na tawagar Denmark yana da sauran shekara daya a kwantiraginsa da kungiyar amma zai iya tafiya idan an saye shi a kudin da ya kai fam miliyan 70 kamar yadda jaridar (Mail) ta labarto.

United tana harin sayen dan wasan kungiyar Lille ta Faransa kuma dan tawagar Ivory Coast Nicolas Pepe, mai shekara 24, wanda aka yi masa kudi fam miliyan 24, domin maye gurbin dan wasanta na gaba, dan Belgium Romelu Lukaku, idan har ya tafi Inter Milan, in ji (Times)

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Idrissa Gueye ya taka rawar gani sosai a Everton

Dan wasan tsakiya na Lazio kuma na tawagar Serbia Sergej Milinkovic-Savic, mai shekara 24, ya gaya wa abokan wasansa a kungiyar cewa zai bar kulob din na Italiya a kakar bana yayin da ake rade-radin tafiyarsa Manchester United, kamar yadda (Il Tempo via Express) ta ruwaito.

Su kuwa kungiyoyin Jamus biyu Wolfsburg da RB Leipzig suna sha'awar karbo matashin dan wasan Arsenal ne mai shekara 18, dan Ingila Emile Smith Rowe, in ji (Independent)

Barcelona ta kara tayin da ta yi wa dan wasan baya na Real Betis, na tawagar Sifaniya ta 'yan kasa da shekara 21 Junior Firpo, zuwa fam miliyan 24, in ji (Sport)

Chelsea da West Ham na harin sayen dan wasan gaba na gefe na Portsmouth, Leon Maloney mai shekara 18, wanda ya ci bal 26 a tawagar matasan kungiyar a kakar da ta wuce, in ji (Sun)

Labarai masu alaka