Juve na neman Neymar, United na son Maguire

Gareth Bale Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce ba zai bata lokaci ba kan Gareth Bale

Manchester United na shirin rabuwa da Paul Pogba na Faransa mai shekara 26, yayin da take dab da cimma yarjejeniya da Lazio kan dan wasan Serbia Sergej Milinkovic-Savic, 24 akan kudi £70m. (Mirror)

Sai dai, akwai yiyuwar Pogba zai ci gaba da taka leda a Old Trafford akalla na tsawon kaka daya, wanda hakan kan iya zama matsala ga kokarin United na karbo Milinkovic-Savic. (Express)

Manchester United kuma za ta runtse ido ta saye dan wasan Leicester City Harry Maguire kan fam £80m bayan dan wasan bayanta Eric Bailly ya samu rauni a guiwarsa a wasan sada zumunci da Tottenham. (Mirror)

An fada wa Manchester United cewa sai ta kashe fam miliyan £30m kan dan wasan Newcastle mai shekara 21 Sean Longstaff. (Labaran Manchester na yamma)

Dan wasan Lyon Moussa Dembele zai kasance cikin jerin 'yan wasan da Manchester United za ta mayar da hankali akai idan har ta sayar da Romelu Lukaku, mai shekara 26. (Sky Sports)

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya yi watsi da bukatar dan wasan gaba na Real Madrid Gareth Bale mai shekara 30, inda ya ce ya fi mayar da hankali kan gina tawagarsa maimakon wani dan wasa. (Independent)

Everton ta shaida wa Crystal Palace cewa a shirye ta ke ta biya fam miliyan £60m hadi da dan wasanta na Turkiya Cenk Tosun domin karbar Wilfried Zaha, mai shekara 26, saboda shakkun da take yi Chelsea na iya karbe dan wasan. (Telegraph)

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Neymar ya fi kaunar ya koma Barcelona

Juventus da dan wasanta Cristiano Ronaldo mai shekara 34 sun gaza shawo kan Neymar na Paris St-Germain zuwa kulub din na Seria A, saboda dan wasan na Brazil ya fi karkata ya koma tsohuwar kungiyarsa Barcelona. (Star)

Borussia Dortmund na tattaunawa da Barcelona game da Malcom kan kudi fam miliyan £37.5m. (Goal)

Kocin Napoli Carlo Ancelotti yana nan kan bakarsa ta sayen dan wasan Colombia James Rodriguez mai shekara 28 daga Real Madrid kafin rufe kasuwar musayar 'yan wasa. (Marca)

Labarai masu alaka