Xavier Amaechi ya bar Arsenal zuwa Hamburg

Xavier Amaechi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona, Bayern Munich, Inter Milan da wasu kungiyoyin Firimiya sun nemi Amaechi a baya

Dan wasan gefe na Arsenal Xavier Amaechi ya koma Hamburg inda ya sa hannu kan kwantiragin shekara hudu a kulob din na Jamus da ke matakin Lig na biyu.

Hamburg za su biya kudin da ya kai fam miliyan 2.25, da kuma wasu karin miliyoyi idan dan kwallon ya yi kokari, sai dai ba dole ba ne a sake sayarwa da Arsenal shi nan gaba.

Dan kwallon na tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 18, wanda tuni aka gwada lafiyarsa, zai sa lamba 17.

Barcelona, Bayern Munich, Inter Milan da wasu kungiyoyin Firimiya sun nemi Amaechi a baya amma ya ki yarda.

  • v

Labarai masu alaka