Dani Alves na neman kulub, Ina Lukaku zai koma?

Dani Alves na Brazil Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dani Alves ya dade yana taka leda a manyan kungiyoyi

Tsohon dan wasan Barcelona da Paris St-Germain Dani Alves, har yanzu yana neman sabuwar kungiya, inda ya fito a Instagram yana neman a taimaka ya samu kungiyar da zai taka leda, in ji (AS)

Dan wasan gaba na Manchester United Romelu Lukaku watakila ya nuna alamun yana dab da yin bankwana da Old Trafford nan ba da dadewa ba bayan wallafa hoto da wakilinsa a shafinsa na Twitter.

Dan wasan na Belgium ya nuna cewa suna aiki kan makomarsa "nan ba da dadewa", kamar yadda (Manchester Evening News) ta rawaito.

Tsohon kocin Manchester United Sir Alex Ferguson yana son kulub din ya karbo dan wasan tsakiya na Aston Villa dan kasar Scotland John McGinn - wanda kakansa abokin Farguson ne, in ji (Sun).

Kocin Leicester City Brendan Rodgers ya ce har yanzu Manchester United da Manchester City da suka nuna sha'awar dan wasansa na baya Harry Maguire ba su taya shi yadda ya kamata ba, a cewar (Leicester Mercury).

Kocin Everton ya ce har yanzu ba su cimma yarjejeniya ba da Paris St-Germain kan dan wasan Senegal Idrissa Gueye, inda kocin ke fatan dan wasan zai ci gaba da taka leda a Goodison Park, in ji (Liverpool Echo).

Ko da yake ana tunanin Gueye zai tafi Paris a ranar Lahadi domin duba lafiyar shi, bayan ya yi watsi da tayin Manchester United, in ji (Daily Express).

Sabon kocin Chelsea Frank Lampard ya shaida wa 'yan wasan tsakiya na kungiyar guda biyu Tiemoue Bakayoko da Danny Drinkwater cewa za su iya barin kungiyar, wadanda farashinsu su biyu ya kai fam miliyan £80m, a cewar (Mirror).

Labarai masu alaka