Gareth Bale zai ci gaba da zama a Madrid

Gareth Bale Hakkin mallakar hoto Getty Images

Real Madrid ta hana shirin da Gareth Bale ke yi na komawa kungiyar Jiangsu Suning ta China domin ci gaba da taka-leda.

Tun farko an sa ran Bale, dan kwallon tawagar Wales zai koma buga gasar China kan yarjejeniyar shekara uku kan fam miliyan daya da zai dunga karba kowanne mako.

A can baya kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya fayyace cewar Bale ba ya cikin tsarinsa, kuma yana fama da jinyar rauni, domin wasan La Liga 79 ya buga a kaka hudu da ya yi a Bernabeu.

A makon jiya Zidane ya ce Bale ya kusan barin Real, kuma hakan zai amfani dan wasan da kungiyar da zai koma da ita Madrid din gabannin karawar sada zumunta da Bayern Munich.

Hakan ne ya sa Real ya maida hankali kan kudin da za ta sayar da Bale ga duk kungiyar da take bukatar daukar shi a bana.

Bale ya koma Real Madrid a 2013 kan fam miliyan 85, a matsayin mafi tsada a duniya, ya kuma taimakawa kungiyar ta lashe kofin Zakarun Turai hudu a zamansa a Bernabeu.

Dan wasan tawagar Wales ya buga wa Real wasa biyu na atisayen tunkarar kaka mai zuwa, inda ya ci kwallo a wasan da suka yi 2-2 da Arsenal.

Haka kuma ya buga minti 30 a karawar da Atletico Madrid ta doke Real Madrid 7-3 a wasan hamayya a dai atisayen tunkarar kakar bana.

Wakilin Bale a harkokin tamaula, Jonathan Barnet ya bayyana Zidane a matsayin mara kirki kan yadda ya dauki bakun Bale, ya kuma ce duk cinikin da za su yi sai dai ya amfani wanda yake wakilta.

Labarai masu alaka