Lyon ta ci Arsenal a wasan atisayen tunkararar kakar bana a Emirates Cup

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar Lyon ta doke Arsenal da ci 2-1 a wasan karshe a Emirates Cup, a karawar atisayen tunkarar kakar kwallon kafa ta bana.

Pierre-Emerick Aubameyang ne ya fara cin kwallo tun kan aje hutu, kuma kayatatcen kwallo ya zura a ragar Lyon.

Bayan da aka dawo ne kungiyar ta Faransa ta kara kaimi ta kuma farke kwallo, sannan ta kara na biyu dukka ta hannun Moussa Dembele.

Matashin dan wasan Arsenal, Gariel Martinelli ya ci wata kwallo inda ya fara murna daga baya aka ce ya yi satar gida.

Karon farko da Martinelli ya buga wa Arsenal tamaula kuma a filin Emirates, bayan da aka koma daga hutu tare da shi ma sabon zuwa Gunners, Dani Ceballos wanda zai yi mata wasannin aro daga Real Madrid.

Arsenal ta kulla yarjejeniyar daukar dan wasan Lille, Nicolas Pepe kan fam miliyan 72, inda wasu ke tunanin makomar Henrikh Mkhitaryan a Arsenal idan aka kammala cinikin.

Henrikh Mkhitaryan ya koma Arsenal daga Manchester United a Janairun 2018, ya kuma taka-rawar gani a karawa da Lyon.