Kano Pillars ta lashe Aiteo Cup

Hakkin mallakar hoto Pillars fan

Kano Pillars ta yi nasarar lashe kofin kalubale na Najeriya wato Aiteo Cup na bana.

Pillars ta yi nasara ne a kan Niger Tornadoes a bugun fenariti da ci 4-3, bayan da suka tashi wasa babu ci a filin wasa na Ahmadu Bello da ke jihar Kaduna, Najeriya.

Bayan da aka fara bugun fenariti Pillars ce ta fara buga wa ta kuma ci, itama Tornadoes ta buga nata ta jefa a raga.

Daga nan ne Madaki na Kano Pillars ya barar da tashi, dan wasan Tornadoes Mohammed Hussain shima bai ci ba.

Fenariti dai na 1-1 sai Adamu Hassan na Pillars ya buga shima ya kasa ci, nan da nan dan kwallon Tornadoes Ruben ya karbi tamaula ya ajiye ya buga amma sai ta yi sama.

Sauran 'yan wasa bibiyu daga kowanne bangare wato Bature da Victor kowanne ya ci kwallo, haka ma na Tornadoes Denis da Obinna kowa ya ci tasa 3-3 kenan.

Sai dan wasa Pillars, Emmanuel Anyawu ya buga ta shiga raga, yayin da dan wasan Tornadoes Ayo Adebola ya barar da tasa, wasa ya tashi 4-3.

Wannan ne karon farko da Pillars ta lashe kofin kalubalen Najeriya tun bayan 1953, lokacin da Kano ta doke Lagos Dynamos da ci 2-1.

Ko a bara ma sai da Pillars ta kai wasan karshe inda ta ci Rangers 3-0 kan a tashi aka farke kwallayen aka kuma fitar da ita a bugun fenariti.

Pillars wadda ta yi ta biyu a gasar Premiyar Nigeria, za ta wakilci kasar a gasar cin kofin Zakarun Afirka a bana, inda za ta fara karbar bakuncin Ashante Kotoko ta Ghana.

Hakkin mallakar hoto LMCNPL

Tun kan wasan Pillars din an tashi karawa babu ci a wasn karshe na kofin kalubalen na mata tsakanin Nasarawa Amazons da Rivers Angels.

Shima a bugun fenariti aka samu gwarzuwar bana, inda Nasarawa Amazons ta lashe kofin da ci 5-4,