Lacazette ya ce da shi za a fara Premier

aRSENAL Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasan Arsenal, Alexander Lacazette ya ce yana da tabbaci cewar da shi za a fara wasannin cin kofin Premier kakar bana.

Lacazette ya yi rauni ne a karawar da Lyon ta doke Arsenal da ci 2-1 a Emirates Cup ranar Lahadi.

Likitocin Gunners na auna girman raunin da ya yi, har ma sun ce ba wani mai muni bane.

Hakan ya kwantar da hankali koci Unai Emery, har ma ya yi fatan dan wasan mai shekara 28, ba zai yi doguwar jinya ba.

Hakan na nufin dan kwallon tawagar Faransa ba zai yi wa Arsenal karawar sada zumunta da za ta yi da Angers a Faransa ranar Laraba ba.

Arsenal wadda karo na uku a jere bata cikin 'yan hudun farko a gasar Premier, za ta ziyarci Newcastle United ranar Lahadi 11 ga watan Agustan 2019.

Wasannin Premier bana da za a fara kakar bana

Juma'a 9 Agusta 2019

  • Liverpool da Norwich City

Asabar 10 Agusta 2019

  • West Ham United da Manchester City
  • Watford da Brighton & Hove Albion
  • Burnley da Southampton FC
  • Crystal Palace da Everton
  • Bournemouth da Sheffield United
  • Tottenham da Aston Villa

Lahadi 11 Agusta 2019

  • Newcastle United da Arsenal
  • Leicester da Wolverhampton Wanderers
  • Manchester United da Chelsea

Labarai masu alaka