Leroy Sane zai koma Bayern, Matuidi na son zuwa Man United

Bruno Fernandes na Sporting Lisbon Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manchester United za ta duba lafiyar Bruno Fernandes na Sporting Lisbon

Kocin Bayern Munich Niko Kovac yana da cikakken fatan cewa za su kammala yarjejeniya da dan wasan gaba na Manchester City Leroy Sane, mai shekara 23, in ji jaridar ZDF Sport daga Manchester Evening News.

City har ta fara nazarin karbo Mikel Oyarzabal daga Real Sociedad domin maye gurbin Sane idan har tafiyarsa ta tabbata, in ji jaridar AS.

Shugaban Real Madrid Florentino Perez ya bar Gareth Bale cikin 'fushi' kan matakinsa na jingine komawar dan wasan na Wales kungiyar Jiangsu Suning ta China, in ji Sun

Perez na ganin tsohon dan wasan na Tottenham yana da darajar da ba za a iya hasarar shi ba, a yayin da Jiangsu Suning ke shirin karbar dan wasan, a cewar Daily Star.

Dan wasan Sporting Lisbon Bruno Fernandes zai tafi Ingila domin duba lafiyar shi a Manchester United, in ji Daily Express.

A ranar Talata ko Laraba ake sa ran Arsenal za ta kammala cinikin dan wasan Lille Nicolas Pepe, mai shekara 24, idan har Paris St-Germain ba ta kwace dan wasan ba. (La Voix Du Nord)

Dan wasan tsakiya na Juventus Blaise Matuidi, mai shekara 32, ya nuna sha'awar yana son komawa Manchester United. (Corriere di Torino via Daily Express)

Everton ta taya dan wasan Crystal Palace Wilfried Zaha kan fam miliyan 55, kudi hannu, ba tare da karin wani dan wasa ba, in ji Sky Sports.

Palace tana son Everton ta biya fam miliyan £60m kan dan wasan na Ivory Coast, mai shekara 26, a cewar Daily Mirror.

Dan wasan Everton Idrissa Gueye na Senegal mai shekara 29, ya isa Paris inda yake dab da zama dan wasan Paris St-Germain, in ji (RMC Sport ta hannun Liverpool Echo).

Labarai masu alaka