PSG ta dauki Idrissa Gueye daga Everton

Idrissa Gueye Hakkin mallakar hoto Getty Images

Paris Saint-Germain ta sanar da cewar ta kammala daukar dan kwallon Everton, Idissa Gueye.

Dan kwallon tawagar Senegal, mai shekara 29, ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta kare a karshen kakar 2023, amma ba a fayyace kudin da aka saye shi ba.

PSG ta yi zawarcin dan wasan wanda ya buga wa Senegal gasar kofin nahiyar Afirka a Masar, wanda ta so ta saya a watan Janairu, an kuma alakanta shi da zuwa Manchester United a lokacin.

Dan kwallon ya buga wasa kaka bakwai a Lille daga 2008 zuwa 2015 daga nan ya koma Ingila tare da kungiyar Aston Villa wadda ya yi wa wasa 108 a kaka uku da ya yi.

Labarai masu alaka