Man United na son Dybala, Arsenal za ta dauki Tierney

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Manchester United tana shirin gabatar da bukatarta ta daukar Paulo Dybala mai shekara 26 daga Juventus.

Jaridar Marca ta ruwaito cewa Paris St-Germain ta ki yarda da komawar Neymar mai shekara 27 zuwa Barcelona.

Amma Express ta ruwaito cewa jami'an PSG din za su gana da na Barcelona domin samo hanyar da za a cimma yarjejeniya tsakanin kungiyoyin biyu.

Manchester United na sha'awar daukar dan wasan bayan Barcelona kuma dan kasar Faransa Samuel Umtiti mai shekara 25, in ji Le10 Sport.

Arsenal na dab da daukar dan wasan baya mai buga bangaren hagu na kungiyar Celtic wato Kieran Tierney mai shekara 22, a rahoton jaridar Mail.

Hakkin mallakar hoto Mark Runnacles

Mauro Icardi na Inter Milan mai shekara 26 zai iya koma wa Napoli kan kudi fan miliyan 73, kamar yadda Corriere dello Sport ta ruwaito.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasan Juventus Moise Kean mai shekara 19 ya zabi koma wa Everton a kan Arsenal ne saboda Arsenal din ba za ta ba shi damar buga wasanni ba a babbar kungiyarta, in ji Mail.

Babban jami'in kulob din Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge ya ce bai fahimci dalilin da ya sa kocin kungiyar, Niko Kovac ya ke da kwarin gwiwar daukar Leroy Sane ba daga Manchester City. (Bild)

Zinedine Zidane ya ce ba shi da tabbacin ko dan wasan kasar Colombia James Rodriguez zai ci gaba da kasancewa a Real Madrid a kaka ta gaba. Marca ce ta ruwaito.

Mahaifin dan wasan bayan Arsenal Shkodran Mustafi da kuma wakilinsa sun kawar da yiwuwar komawar dan wasan mai shekara 27 zuwa wani kulob a Italiya, a cewar rahoton Romanews.

Crystal Palace ta mika tayin kusan fan miliyan 14 ga CSKA Moscow domin daukar dan wasanta mai shekara 21 mai suna Fedor Chalov, in ji Sky Sports.

Har wa yau, Sky din ta ruwaito cewa Jose Mourinho zai dawo fagen horar da tamaula idan ya samu dama mai kyau.

Dan wasan tsakiyar Atletico Madrid Koke ya ce matashin dan wasan gaban kungiyar Joao Felix zai zama "daya daga cikin mashahuran 'yan wasa a duniya". (ESPN)

Labarai masu alaka