United za ta ci tarar Lukaku kan kin zuwa atisaye

United Hakkin mallakar hoto Getty Images

Manchester United za ta ci tarar Romelu Lukaku, bayan da dan wasan bai halarci atisaye ba tare da izini ba.

Dan wasan tawagar Belgium ya yi atisaye a tsohuwar kungiyarsa Anderlecht kwana biyu da suka wuce, koda yake Litinin ranar hutu ce ga 'yan wasan United.

Mai kula da harkokin tamaular Lukaku ya je Landan domin warware matsalar.

Kungiyoyin da ke buga Serie A, Inter Milan da Juventus na son sayen Lukaku mai shekara 26, wanda bai buga wa United wasannin atisayen tunkarar kakar bana ba, sakamakon jinya.

Federico Pastorello zai yi zama da mahukuntan United da na Inter Milan don cimma matsaya kan Lukakun.

Kungiyoyin Italiya na son rage farashin da United ta yi wa dan kwallon, wadda ta nace a biyata fam miliyan 75 kudin da ta sayo Lukaku daga Everton shekara biyu baya.

A watan Yuli kungiyoyin Italiya suka taya dan kwallon fam miliyan 54, wanda Manchester ta sa ran zai koma Old Trafford ranar Talata, amma bai je ba kuma bai tambayi izini ba..

Labarai masu alaka