Premier: Man City da Tottenham da Liverpool sun fara da kafar dama

Brighton ya gaza lashe wasanninta 9 da suka gabata na Premier Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Brighton ya gaza lashe wasanninta 9 da suka gabata na Premier

Manchester City ta fara farautar lashe kofin Premier karo uku a jere bayan ta caccasa West Ham a ranar farko na soma gasar a bana.

Na'urar VAR da aka fara amfani da ita a karon farko a gasar Premier, ta taka rawa sosai ga nasarar da City ta samu inda lallasa West Ham ci 5-0.

Kwallaye uku rigis Raheem Sterling ya jefa, yayin da Gabriel Jesus da Sergio Aguero, suka ci sauran kwallayen a bugun fanariti.

Harry Kane kwallaye biyu ya ci wanda ya taimaka Tottenham doke Aston Villa ci 3-1. Aston Villa ce ta cin Tottenham ta kafar John McGinn, kafin daga bisani Tanguy Ndombele, ya farke wa Tottenham.

Ana saura minti hudu a hure wasan, Kane ya zira kwallaye biyu.

Sheffield United, da ta hauro gasar Premier a bana bayan shekara 12 ta yi 1-1 ne da Bournemouth. Haka ma Everton, ta tashi babu ci tsakaninta da Crystal Palace.

Brighton, da ta sha da kyar a Premier a bara ta fara da kafar dama a bana inda ta casa Watford 3-0. Haka ma Burnley ta doke Southampton, ci 3-0.

Wasanni uku za a buga ranar Lahadi, ciki har da gwabzawa tsakanin Manchester United da Chelsea a Old Trafford.

Karon farko kenan da Frank Lampard zai jagoranci Chelsea a gasar Premier.

Labarai masu alaka