Chelsea za ta sayo dan wasan baya, Roma na zawarcin Dejan Lovren

A Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manchester United ta doke Chelsea da ci 4-0 ranar Lahadi

Kocin Chelsea Frank Lampard yana son ya sayo dan wasan bayan Leicester City Ben Chilwell lokacin da aka dage wa kungiyarsa haramcin sayan sabbin 'yan wasa. An yi wa dan wasan Ingilan farashin fan miliyan 70 ne, a cewar jaridar Sun.

AS Roma tana neman dan wasan Liverpool da Croatia Dejan Lovren, mai shekara 30, in ji (Corriere dello Sport - in Italian).

Dan wasan Faransa Paul Pogba, mai shekara 26, ya ce "babu wata alamar tambaya" dangane da makowarsa a Manchester United, in ji (RMC - in French).

Barcelona ta ce Philippe Coutinho ba zai bar kungiyar ba a kakar bana, kamar yadda kafar yada labarai ta (Marca) ta ruwaito.

Tattaunawa tsakanin Barcelona da Paris St-Germain game da musayar Neymar ta samu cikas bayan da PSG ta nemi Barca ta ba ta wasu 'yan wasa uku bayan ta biya ta kudin dan wasan mai shekara 27, a cewar (Sport).

Wakilan dan wasan Arsenal Mesut Ozil, mai shekara 30, za su tafi Amurka don tattaunawa da kungiyar DC United dangane da yiwuwar komawar tsohon dan wasan Jamus din can, kamar yadda kafar yada labarai ta (Express) ta ruwaito.

Labarai masu alaka