PSG ta ki sallama Neymar ga Barca ko Real

PSG Hakkin mallakar hoto Getty Images

Paris St Germain ta ki sallama tayin da Barcelona da Real Madrid suka yi wa dan kwallon tawagar Brazil, Neymar.

Barcelona ta taya tsohon dan wasanta fam miliyan 92.4, sannan za ta hada mata da Philippe Coutinho.

An kuma ambaci bayar da Ivan Rakitic ga PSG a cikin tayin da ta yi wa dan kwallon tawagar Brazil mai shekara 27.

Ita ma Real Madrid ta taya Neymar kudi mai tsoka da bayar da 'yan wasanta Gareth Bale da kuma James Rodriguez.

Sai dai kuma PSG ta ce tana bukatar a hada mata da Vinicius Junior, amma dai Real ba ta ce za ta bayar da dan kwallon ba.

Babu tayin da aka amince da shi kawo yanzu, amma ana jin PSG za ta zabi yin ciniki da Real maimakon Barcelona kungiyar da ta sayo Neymar.

Neymar ya zama dan kwallon da ya fi tsada a duniya a 2017, inda PSG ta biya fam miliyan 205, kuma shi ne ya biya sauran kunshin kwantiraginsa a Camp Nou.

Dan wasan ya ci kwallo 34 a kaka biyu da ya yi a Faransa, koda yake ya sha fama da jinya.

A ranar Lahadi magoya bayan PSG suka daga wani kyalle mai dauke da sako ga Neymar cewar ''Kai tafiyarka'', a wasan farko na Ligue 1 da ta yi da Nimes.

Labarai masu alaka