Messi da Ronaldo da Virgil Gwarzon UEFA 2019

UEFA best player 2019 Hakkin mallakar hoto Getty Images

Lionel Messi da Cristiano Ronaldo suna cikin 'yan wasan da ke takarar gwarzon dan kwallon kafa na Turai na bana.

Shi ma dan wasan Liverpool, Virgil van Dijk yana cikin 'yan takarar kyautar da Luka Modric ya lashe a bara.

A bangaren mata kuwa 'yar wasan tawagar Ingila ta mata, Lucy Bronze da mai taka-leda a Lyon Ada Hegerberg da Amandine Henry suna cikin takarar shekarar 2018-19.

Dan kwallon Barcelona da tawagar Argentina, Messi ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar Turai karo uku, shi kuwa dan wasan Juventus da Portugal, Ronaldo ya zama zakara sau hudu tun daga shekarar 2008.

Van Dijk shi ne ya lashe kyautar fitaccen dan wasan Premier da kungiyar kwararrun 'yan kwallo ta karrama shi a 2018-19, ya kuma taimaka wa Liverpool cin Champions League a watan Yuni da UEFA Super Cup ranar Laraba.

Ita kuwa Bronze ta taimaka wa Ingila kai wa daf da karshe a gasar kofin duniya ta mata da aka yi a Faransa a bana wanda Amurka ta lashe kuma karo na biyu a jere.

Hegerberg ita ce ta lashe kyautar gwarzuwar 'yan kwallon kafa a 2016, ita kuwa Henry wannan ne karo na biyar tana yin takara.

Ranar Alhamis 29 ga watan Agusta za a bayyana gwarzon dan kwallon kafa na Turai na baya a Monaco lokacin da za a gudanar da jadawalin wasannin Champions League.

Labarai masu alaka