Sanchez ya ki barin Man Utd, Coutinho zai koma PSG

Alexis Sanchez Hakkin mallakar hoto Getty Images

Alexis Sanchez ya fasa barin Manchester United a kakar bana, duk da cewa kocin kungiyar Ole Gunner Solskjaer ya yi barazanar ajiye shi a benci, ita kuma Roma wadda take zawarcinsa ta koma neman wasu 'yan wasan, in ji jaridar Sun.

Sai dai kungiyar AC Milan da Juventus da kuma Napoli sun nuna sha'awarsu ga dan kwallon na Chile, kamar yadda jaridar Mail ta ruwaito.

Real Madrid ta ki amincewa da bukatar Paris St-Germain ta neman a hada mata da Vinicius Junior, mai shekara 19, kafin ta mika mata dan wasan Brazil, Neymar, mai shekara 27, a cewar AS.

Bayan Vinicius, PSG tana son Madrid ta kara mata da Luka Modric, mai shekara 33, da dan wasan Brazil Casemiro, mai shekara 27, kafin ta ba ta Neymar, in ji Marca.

Neymar ya yi atisaye ne shi kadai a ranar Laraba kuma zai ci gaba da yin hakan har sai bayan da aka sayar da shi, a cewar Esporte Interactivo, via Mundo Deportivo.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tun da farko PSG ta yi watsi da wani tayi mai tsoka da Barcelona da Real Madrid suka yi wa dan kwallon, kamar yadda jaridar Mirror ta wallafa.

Dan wasan Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 27, zai iya koma wa PSG a wani ciniki na daban da na Neymar, in ji kafar yada labarai ta Goal.

Akwai yiyuwar dan kwallon bayan Ingila Danny Rose, mai shekara 29, ba zai bar Tottenham ba har sai karshen watan Janairun badi, kuma dan wasan zai ci gaba da kasance a cikin 'yan wasa 11 na farko na kungiyar, a cewar (Football.London).

Hakazalika Tottenham ba za su ci gaba da zawarcin dan wasan Juventus, Paulo Dybala, mai shekara 25, duk da cewa dan kwallon yana da muradin barin Italiya, in ji Di Marzio.

Labarai masu alaka