Ahmed Musa ba zai buga wasa da Ukraine ba

Ahmed Musa Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tawagar kwallon kafa ta Najeriya wato Super Eales, za ta buga wasan sada zumunta da ta Ukraine ranar Talata.

Wannan ne karon farko da Super Eagles za ta yi wasa tun bayan mataki na uku da ta yi a gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka yi a Masar tsakanin watan Juni zuwa Yuli.

Cikin wadan da Super Eagles ta je da su Masar da kuma za su buga mata wasan sada zumunta da Ukraine sun hada da mai tsaron raga Francis Uzoho da kuma Ikechukwu Ezenwa,

Akwai kuma masu tsaron baya Olaoluwa Aina da Chidozie Awaziem da Ekong da Leon Balogun da Jamilu Collins da amsu buga tsakiya Alex Iwobi da kuma Etebo .

Sauran sun hada da masu cin kwallo Victor Osimhen da Moses Simon da Samuel Chukwueze da Paul Onuachu da kuma Samuel Kalu.

An kuma je Ukraine tare da mai tsaron baya Bryan Idowu da kuma Oluwasemilogo Ajayi da kuma dan kwallon Leicester City, Kelechi Iheanacho wadan da ba a je da su Masar ba.

Sai dai kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ba zai buga karawar ba, sakamakon jinya da yake yi, bayan shi Kenneth Omeruo da Tyronne Ebuehi da Wilfred Ndidi da kuma Henry Onyekuru ba za su buga wasan ba.

'Yan wasan Super Eagles da aka je da su Ukraine

Masu tsaron raga: Francis Uzoho (Omonia FC, Cyprus) da Ikechukwu Ezenwa (Heartland FC) da kuma Emil Maduka Okoye (Fortuna Dusseldorf, Germany)

Masu tsaron baya: Olaoluwa Aina (Torino FC, Italy) da Chidozie Awaziem (CD Leganes, Spain) da William Ekong (Udinese FC, Italy) da Leon Balogun (Brighton & Hove Albion, England) da Jamilu Collins (SC Padeborn 07, Germany) da Oluwasemilogo Ajayi (West Bromwich Albion, England) da kuma Bryan Idowu (Lokomotiv Moscow, Russia)

Masu buga tsakiya: Alexander Iwobi (Everton FC, England) da Anderson Esiti (PAOK Salonica, Greece) da Oghenekaro Etebo (Stoke City FC, England) da Kelechi Iheanacho (Leicester City, England) da kuma Joseph Aribo (Glasgow Rangers, Scotland)

Masu cin kwallo: Victor Osimhen (Lille OSC, France) da Moses Simon (FC Nantes, France) da Joshua Maja (Girondins Bordeaux, France) da Samuel Chukwueze (Villarreal FC, Spain) da Samuel Kalu (Girondins Bordeaux, France) da Paul Onuachu (KRC Genk, Belgium) da kuma Emmanuel Dennis (Club Brugge, Belgium)

Labarai masu alaka