Kasuwar musayar 'yan wasa: Ibrahim Iriyos ne mafi tsada a Gano

Ibrahim Iriyos

A farkon makon Satumba aka rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon kafa ta nahiyar Turai, musammam Italiya da Faransa da Jamus da kuma Spaniya.

A nahiyar Afirka akan gudanar da cinikayyar 'yan kwallo sai dai kudin da ake sayen dan kwallo ku kusa ba ya kai wadanda ake yi a Turai.

A Najeriya an gudanar da wani ciniki mafi tsada a Gano da ke karamar hukumar Dawakin Kudu, inda Super Stars ta dauki Ibrahim Salisu Iriyos a matsayin mafi tsada a garin.

Super Stars mai buga rukuni na biyu a gasar hukumar kwallon kafa ta jihar Kano ta sayo Ibrahin Iriyos daga Aston Villa ta Gano kan kudi naira dubu biyar daidai da fam 10.86.

Dan wasan mai cin kwallo shi da kansa ya yi sha'awar komawa Super Stars da murza leda ganin tana mataki na sama fiye da kungiyarsa ta Aston Villa Gano.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Idin Gano yadda ya ya cinikin Ibrahin Iriyos daga Aston Villa Gano

Hakan ya sa Iriyos kan je Super Stars atisaye a lokacin da kungiyarsa Aston Villa ke yin hutu, wanda hakan ya sa nan da nan aka amince da yadda yake taka leda aka kuma cimma matsaya a dauko shi.

Idin Gano shi ne shugaban Super Stars wanda ya je wajen kocin Aston Villa, Abba Alasan Isa wanda ake kira Abba Goma suka cimma matsaya kan farashin Ibrahim Iriyos.

Ga cinikayya da aka yi a manyan kasashen da suke kan gaba a tamaula a Turai a bana.

Gasar La Liga, Spaniya

An yi hada-hada 398 an kuma kashe sama da fan biliyan 1.70.

Wadanda aka saya mafi tsafa sun hada da:

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Joao Felix, dan wasan gaba, daga Benfica zuwa Atletico Madrid kan fan miliyan 113.

Antoine Griezmann, dan wasan gaba, daga Atletico Madrid zuwa Barcelona kan fan miliyan 107.6

Eden Hazard, dan wasan gaba, daga Chelsea zuwa Real Madrid kan fan miliyan 88.5

Gasar Serie A ta Italiya

An yi hada-hada 516 kan kudi fan biliyan 1.38

Wadanda aka saya mafi tsada:

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Romelu Lukaku, dan gaba, daga Manchester United zuwa Inter Milan kan fan miliyan 70

Matthijs de Ligt mai tsaron baya daga Ajax zuwa Juventus kan fan miliyan 67.8

Joao Cancelo mai tsaron baya daga Juventus zuwa Manchester City kan fam miliyan 60

Gasar Bundesliga, Jamus

An yi hada-hada 287 an kuma kashe fan miliyan 923.3

Wadanda aka saya mafi tsada:

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Lucas Hernandez mai tsaron baya daga Atletico Madrid zuwa Bayern Munich kan fan miliyan 68.

Luka Jovic, dan gaba, daga Eintracht Frankfurt zuwa Real Madrid kan fan miliyan 57.7

Sebastien Haller, dan gaba, daga Eintracht Frankfurt zuwa West Ham United kan fan miliyan 40.7

Gasar Premier, Ingila

An yi hada-hada 526 kan fan biliyan 1.83

Wadanda aka saya mafi tsada:

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Eden Hazard, dan gaba, daga Chelsea zuwa Real Madrid kan fan miliyan 88.5

Harry Maguire, mai tsaron baya, daga Leicester City zuwa Manchester United kan fan miliyan 80

Nicolas Pepe, mai buga gefe, daga Lille zuwa Arsenal kan fan miliyan 72

Labarai masu alaka