Kudin 'yan kwallon City ya haura Yuro biliyan daya

Man cITY Hakkin mallakar hoto BBC Sport
Image caption City ce ta farko da ta lashe Premier a jere tun bayan shekara 10 da Manchester United ta yi hakan

Manchester City ita ce kungiya ta farko da ke da 'yan wasa da kudinsu jumulla ya kai sama da Yuro biliyan daya in ji wani rahoto da CIES mai sa ido da bincike a harkar kwallon kafa ya fitar.

Tun bayan da rukunin kamfanin Abu Dhabi ya sayi Manchester City a 2008, ya kashe Yuro biliyan 1.01 wato fam miliyan 906 wajen hada 'yan kwallon da suke a yanzu.

'Yan wasan da suke buga wa Paris St Germain tamaula kudin su ya kai Yuro miliyan 913 da Real Madrid mai 'yan kwallo da kudin su ya kai Yuro miliyan 902 a mataki na uku in ji CIES.

City wadda ta lashe kofin Premier a bara, tana da 'yan wasan da kudinsu ya kai linkin na 'yan kwallon Norwich sau 32.

A Ingila, Manchester ce ta biyu wadda 'yan wasanta kudinsu ya ka kai Yuro miliyan 751.

Latsa nan don ganin jerin kungiyoyin da ke da 'yan wasa masu tarin kudi

Kamfanin CIES mai yin bincike da kididdiga a fannin kwallon kafa da ke Switzerland, ya gudanar da bincikensa kan manyan 'yan kwallo da ke kowacce kungiya da ke buga manyan gasar Turai wato Premier da La Liga da Serie A da kuma Bundesliga.

Binciken ya ce Paderborn wadda ta samu gurbin buga gasar Bundesliga a bana, ita ce mafi karanci da ke dauke da 'yan wasa da kudin su ya kai fam miliyan 3.57.

Ga jerin 10 da ke sawun gaba a kudi na Yuro

1. Manchester City - Biliyan 1.014

2. Paris St-Germain - Miliyan 913

3. Real Madrid - Miliyan 902

4. Manchester United - Miliyan 751

5. Juventus - Miliyan 719

6. Barcelona - Miliyan 697

7. Liverpool - Miliyan 639

8. Chelsea - Miliyan 561

9. Atletico Madrid - Miliyan 550

10. Arsenal - Miliyan 498

Wasu da aka zakulo

11. Everton - Miliyan 486

12. Tottenham Hotspur - Miliyan 465

19. Leicester City - Miliyan 312

21. West Ham United - Miliyan 259

Labarai masu alaka