Super Eagles ta yi sake a Ukraine

Super Eagles Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tawagar kwallon kafa ta Ukraine da ta Super Eagles sun tashi wasan sada zumunta 2-2 a fafatawar da suka yi ranar Talata.

Super Eagles wadda ta bakunci Ukraine ce ta fara cin kwalo ta hannun Joe Aribo minti hudu da fara wasa, sannan ta kara ta biyu a bugun fenariti da Victor Osimhen ya buga.

Haka kuma aka je hutu Najeriya da kwallo biyu a raga, ita kuwa mai masaukin baki Ukraine na nema.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne mai masaukin baki ta zare kwallo daya ta hannun Oleksandr Zinchenko, kuma saura minti 10 a tashi daga karawar ta kara zare na biyu ta hannun Roman Yaremchuk.

Kasashen biyu sun buga wasan sada zumuntar ne, bayan da Ukraine ke hutun buga wasannin neman shiga gasar Turai ta 2020.

Ita kuwa Najeria ba ta buga karawar neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar ba, bayan hutu da ta yi a lokacin da hukumar kwallon kafa ta duniya ta ware.

Sai dai kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa bai buga karawar ba, sakamakon jinya da yake yi,

Wannan ne karon farko da Super Eagles ta yi wasa tun bayan mataki na uku da ta yi a gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka yi a Masar tsakanin watan Juni zuwa Yuli.

Jerin 'yan wasan da Super Eagles ta je da su Ukraine

Masu tsaron raga: Francis Uzoho (Omonia FC, Cyprus) da Ikechukwu Ezenwa (Heartland FC) da kuma Emil Maduka Okoye (Fortuna Dusseldorf, Germany)

Masu tsaron baya: Olaoluwa Aina (Torino FC, Italy) da Chidozie Awaziem (CD Leganes, Spain) da William Ekong (Udinese FC, Italy) da Leon Balogun (Brighton & Hove Albion, England) da Jamilu Collins (SC Padeborn 07, Germany) da Oluwasemilogo Ajayi (West Bromwich Albion, England) da kuma Bryan Idowu (Lokomotiv Moscow, Russia)

Masu buga tsakiya: Alexander Iwobi (Everton FC, England) da Anderson Esiti (PAOK Salonica, Greece) da Oghenekaro Etebo (Stoke City FC, England) da Kelechi Iheanacho (Leicester City, England) da kuma Joseph Aribo (Glasgow Rangers, Scotland)

Masu cin kwallo: Victor Osimhen (Lille OSC, France) da Moses Simon (FC Nantes, France) da Joshua Maja (Girondins Bordeaux, France) da Samuel Chukwueze (Villarreal FC, Spain) da Samuel Kalu (Girondins Bordeaux, France) da Paul Onuachu (KRC Genk, Belgium) da kuma Emmanuel Dennis (Club Brugge, Belgium)

Labarai masu alaka