Messi ka iya koma wa Amurka a badi

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A yanzu Messi na da damar barin Barca a karshen kowace kaka

Lionel Messi ka iya barin Barcelona zuwa MLS ta kasar Amurka, kamar yadda Mundo Deportivo ta ruwaito.

Tun farko dai shugaban kungiyar Barcelona ya tabbatar da cewa Messi yana da damar barin kungiyar kamar yadda yarjejeniyarsa ta tanada. Saboda haka a kowane lokaci dan wasan zai iya canza kungiya.

Har wa yau, Mundo Deportivo din ta ruwaito Barcelona na yunkurin yi wa Messi tayin sabuwar yarjejeniya, wadda za ta bai wa dan kasar Argentinan mai shekara 32 damar yin ritaya a kulab din.

Jaridar Star kuwa ta ruwaito cewa Manchester United da Manchester City za su kara wurin daukar dan wasan Benfica kuma dan kasar Portugal Florentino Luis mai sherkara 20.

Ita kuwa Sun ta ce Paul Pogba ya kasa koma wa Real Madrid ne saboda kasa cimma yarjejeniya kan kudin daukar nauyi da ya kai fan miliyan 150.

A rahoton Mail kuwa, Real Madrid za ta sake kaddamar da neman daukar dan wasan Ajax Donny van de Beek mai shekara 22 a bazarar badi.

Kocin tawagar Ingila Gareth Southgate ya ce dan wasan gaban Man United Marcus Rashford ba lamba 9 ba ne saboda haka "yana matakin gwaji ne", a cewar Sun.

Liverpool Echo ta ruwaito Virgil van Dijk mai shekara 28 yana mamkin rade-radin cewa za a sabunta yarjejeniyarsa, inda albashinsa zai koma fan 200,000 a duk mako.

Chelsea ba ta da wani zabi illa ta bijiro da tattaunawa tare da dan wasan bayanta Emerson Palmieri yayin da Maurizo Sarri yake son dauke dan kasar Brazil din zuwa Juventus. (Express)

Mirror ta ce mai tsaron ragar Jamus da kuma Bayern Munich Manuel Neuer, mai shekara 33, ba shi da niyyar yin ritaya daga wasa.

Labarai masu alaka