Fifa 20 ratings: Messi ne kan gaba a Fifa 20 da maki 94

Allon hoton 'yan wasa goman farko a Fifa 20 Hakkin mallakar hoto EA SPORTS FIFA
Image caption Ronaldo ne ya rika jan ragamar kafin yanzu

An fitar da matsayin fitattun 'yan wasan kwallon kafar wasan kwamfuta na Fifa na shekarar 2020 wato Fifa 20.

Akan fito da wasan kwallon kwamfuta na Fifa duk shekara ne, inda ake bai wa kowanne dan wasa sabon matsayi gwargwadon kokarinsa a gasar shekarar da ta gabata.

Fifa 20, wadda ake fitarwa a kowace ranar 24 ga watan Satumba, za ta nuna taurarin 'yan wasa irinsu Eden Hazard da kuma Virgil Van Dijk na Livepool a matsayin fuskar wasannin na Fifa 20.

Sai dai ba su shiga jerin 'yan wasan da suka fi yawan maki ba a sabon jerin sunayen 'yan wasan da aka fitar.

A madadin haka, Lionel Messi shi ne kan gaba cikin wadanda suka fi kowa, inda ya doke tsohon abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo - Messi na kan gaba da maki 94, shi kuma Ronaldo na da maki 93.

Sai kuma fitaccen dan wasa wanda tauraronsa ke haskawa wato Neymar na PSG na biye da su da maki 92, sai Hazard da kuma abokin wasansa a tawagar kasar Belgium wato Kevin De Bruyne.

Bayan wasu 'yan wasanni da mai tsaron ragar Manchester United David De Gea ya yi, inda bai tabuka abin a zo-a-gani ba, yanzu ba shi ne golan da ya fi kowa iya kama kwallo ba.

Jan Oblak na Atletico Madrid ne yanzu ke kan gaba.

Sai dai babu sunayen fitattun 'yan wasa irinsu Harry Kane na Tottenham da Sergio Aguero na Man city da kuma Kylian Mbappe na PSG, wadanda ba sa cikin sunaye goman farko a jerin fitattun, inda kowannensu ke da maki 89.

Fitattun 'yan wasa 10 na Fifa 20:

1) Lionel Messi: 94

2) Crisiano Ronaldo: 93

3) Neymar: 92

4) Eden Hazard: 91

5) Kevin de Bruyne: 91

6) Jan Oblak: 91

7) Virgil van Dijk: 90

8) Mohamed Salah: 90

9) Luka Modric: 90

10) Marc-Andre ter Stegen: 90

Labarai masu alaka