'Firai ministan Isra'ila na neman tayar da zaune tsaye'

Kwarin Jordan na Gabar Yamma Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kwarin Jordan da Netanyahu ke cewa zai kwace ya kai daya bisa uku na yankin Gabar Yamma da kogin Jordan din

Kasashen Larabawa na ci gaba da sukar alkawarin da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya yi cewa, idan aka sake zabensa a mako mai zuwa, zai mayar da yankin Kwarin Jordan, karkashin ikon Isra'ila.

Matakin na nufin Isra'ila za ta kama tare da mamaye wani yanki mai yawa na Gabar Yamma da kogin Jordan kenan.

Kalaman na Netanyahu sun jawo martani tare da harzuka kasashen Larabawa, domin abu ne da suke gani karara na saba doka da neman ta'azzara rashin zaman lafiyar da ake da shi a yankin.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mohammad Shtayyeh ya bayyana Mista Netanyahu a matsayin mai lalata shirin zaman lafiya

Saudi Arabiya ta kira matakin a matsayin mummunar tsokana mai hadari a kan al'ummar Falasdinu, kuma tsabar keta haddi da saba wa dokar ko tanadin majalisar dinkin duniya.

Ita kuwa kungiyar kasashen Larabawa ta Arab League ta bayyana shirin na Mista Netanyahu a matsayin mamaya, yayin da Jordan ta kira shi karin mummunan tashin hankali.

Babban mai shiga tsakani na Falasdinawa Saeb Erakat ya ce shirin, zai kasance laifi ne na yaki, wanda zai binne duk wata dama ta yuwuwar samun zaman lafiya a yankin tsawon shekara dari.

Sai dai Firaministan na Israila ya ce shirin mamayar ba zai hada da birnin Jericho na Falasdinawa ba, ba kuma zai hada da Bafalasdine ko da daya ba.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Benjamin Netanyahu ya kasance Firaministan Isra'ila da ya fi kowanne dadewa a mulki, inda ya zarta na farko David Ben Gurion

A wani matakin mai kama da albishir mista Netanyahu ya bayyana cewa shirin yarjejeniyar Shugaba Trump na sasanta bangarorin biyu na Isra'ila da Falasdiwa wanda ake ta zaman jiran tsammani a gani abin da zai zo da shi, a karshe dai kila ya bayyana 'yan kwanaki kafin zaben.

Ana ganin da alkawarin mamayar na Mista Netanyawun ya yi ne domin dadadawa da samun goyon bayan masu zabensa 'yan ra'ayin rikau, kafin zaben, abin da kuma ake ganin zai iya gamuwa da kakkausar suka daga yawancin kasashen duniya.

Kamar yanda jakadan Falasdinawa a Birtaniya Husam Zomlot shi ma yake cewa ya kamata kasashen duniya su fito su yi watsi da aniyar ta Netanyahu:

Ya ce ''a gare mu Falasdinawa, muna nan a inda muke, za mu ci gaba da zama a cikin kasarmu,, a kan kasarmu, kuma domin kasarmu.Za mu tirji wa duk wani mataki walau na mamayar soja ne ko na wariyar launi.

Magana ce ta alummar duniya, magana ce ta ka'idar bayan yakin duniya na biyu, da kuma ta yaya za mu kare wadannan dokoki, da kuma ta yaya za mu watsi da tashin hankali.

Ba shakka Netanyahu kawai yana da sha'awa ne a kan danniya da cin zali da kuma tashin hankali, kuma mun yi amanna wannan zai kasance mataki mai hadarin gaske a duniya.''