Joe Willcock zai ci gaba da zama a Arsenal

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Willock ya wakilci tawagar matasan Ingila masu shekara 16 da 19 da 20 da kuma 21

Joe Willcock ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Arsenal zuwa lokaci mai tsawo.

Dan wasan tawagar Ingila ta matasa 'yan shekara 21, ya fara zama a Emirates tun yana dan shekara hudu.

Willcock wanda ya fara buga wa Arsenal kwallo a League Cup a karawar da ta yi da Doncaster a Satumbar 2017, ya kuma yi wa Gunners wasan Premier a bana.

Dan wasan mai shekara 20 ya ce ''Arsenal ce a zuciyarsa shi ya sa ya amince ya ci gaba da zama a kungiyar''.

Ya kuma kara da cewar ''kocin kungiyar ya amince da rawar da ya ke yi a Arsenal da sauran matasan da ke buga mata tamaula, kullum ana kara musu kwarin gwiwa a lokacin atisaye''.

Labarai masu alaka