VAR ta yi kuskure hudu a Premier - Riley

VAR Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tsohon babban jami'in alkalancin tamaula, Mike Riley ya ce kawo yanzu VAR ta yi kuskure hudu wajen yanke hukunci a gasar Premier ta bana.

Riley tsohon alkalin wasa kuma daraktan kwararrun alkalai a lokacin wasa, ya gabatar da jawabi a taro da aka yi da masu hanun jari a wasannin Premier a Landan ranar Alhamis.

Riley ya ce akwai fenariti biyu da ya kamata a bai wa Manchester City da West Ham United, kuma bai kamata a karbi kwallon da Newcastle ta ci ba, domin kwallo ta taba hannun dan wasa.

Ya kuma ce ya kamata a bai wa dan kwallon Leicester City, Youri Tielemans fenariti kan ketar da ya yi wa dan wasan Bournemouth, Callum Wilson a karawar da suka yi ranar 31 ga watan Agusta.

Riley ya ce an yi kuskure da ba a bai wa City fenariti a lokacin da dan wasan Bournemouth, Jefferson Lerma ya yi wa David Silva keta a da'ira ta 10 ranar 25 ga watan Agusta.

Ya kuma kara da cewar ya kamata a bai wa West Ham fenariti, bayan da Tom Trybull na Norwich City ya yi wa Sebastien Hallaer keta a da'ira ta 18 ranar 31 ga watan Agusta.

Ya kara da cewar kwallon da Fabian Schar ya ci wa Newcastle a karawa da Watford ranar 31 ga watan Agusta, ta taba hannun Isaac Hayden kan a buga ta shiga raga.

Riley ya ce daga cikin kuskure hudu da ya bayyana, sun duba abubuwan da suka faru a tamaula 227 na yanke hukunci, inda suka yi gyara a guda shida kuma 10 ya kamata su yi.

Ya karkare da cewar VAR, na'urar da take taimakawa alkalin wasa yanke hukunci tana da amfani tana kuma taka rawar gani a yanke hukunci musamman a gasar Premier.

Labarai masu alaka