Madrid na fama da 'yan wasan da ke jinya

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images

Real Madrid ta fara kakar tamaula da jerin 'yan wasanta da ke yin jinya, kuma sai karin wasu take samu da ke yin rauni, bayan da Luka Modric ya shiga sahu.

An duba lafiyar tsohon dan kwallon Tottenham kan raunin da ya yi a kafarsa ta hagun, za kuma a kara duba shi don tantance lokacin da zai yi jinya.

Sai dai Real na fatan dan wasan zai murmure da wuri ganin cewar za ta buga gasar cin kofin Zakarun Turai ta bana da Paris St Germain a wasan farko na cikin rukuni.

Modric ba zai buga wa Real wasan da za ta yi da Levante a gasar La Liga ranar Asabar ba, sai dai ba a sani ba ko zai warke kan gumurzu da PSG.

Dan kwallon ya buga wa tawagar Croatia karawar da ta yi da Azerbaijan ranar Litinin, amma da ya koma Spaniya bai yi atisaye cikin 'yan wasa ba, inda ya shiga dakin motsa jiki.

A masu buga wa Madrid tsakiya, Modric da Isco ba za su yi fafatawar La Liga da Levante ba ranar Asabar, su kuwa Casemiro da Fede Valverde ba su koma Bernabeu da wuri ba ranar Laraba.

Real na fama da 'yan wasa 11 da ke jinya ciki har da fitatcen dan wasan da ta sayo daga Chelsea, Eden Hazrad wanda har yanzu magoya baya na kishirwar rawar da zai taka.

Watan Satumba Real za ta yi wasa biyar a gasar La Liga da kuma kofin Zakarun Turai na Champions League da za ta fafata da PSG.

Cikin karawar Real a watan Satumba har da Sevilla da Osasuna da kuma wasan hamayya da Atletco Madrid, bayan da ta yi 2-2 da Villareal, sannan za ta kara da Levante ranar Asabar.

Labarai masu alaka