Madrid da Chelsea sun cimma yarjejeniya kan Kante

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ngolo Kante ya lashe Premier tare da Chelsea

Real Madrid da Chelsea sun kulla yarjejeniya domin sayen N'Golo Kante, mai shekara 28, inda Chelsesa din za ta ankarar da Madrid idan wata kungiyar ta kawo tayi kan dan wasan tsakiyar Faransar, a cewar rahoton Express.

Akwai yiwuwar Tottenham za ta yi musayar dan wasanta Christian Eriksen, mai shekara 27, da dan wasan gaban Juventus Paulo Dybala, mai shekara 25, a kasuwar sayen 'yan wasa ta watan Janairu mai zuwa. (Express)

Jaridar Sun kuma ta ruwaito cewa Paul Pogba ya amince da albashin fan 429,000 duk mako a Paris St-Germain kafin ranar karshe ta kasuwar sayen wasa. Amma cinikin ya gagara fadawa ne saboda Neymar bai koma Barcelona ba.

Dan wasan da Tottenham ke nema Bruno Fernandes na Sporting Lisbon, mai shekara 25, zai iya komawa kungiyar yayin da Sporting din ta yi masa kudi fan milyan 62, in ji Sport Witness.

Ita kuwa Mirror ta ce kocin Crystal Palace Roy Hodgson ya ce kungiyoyin da suka yi tayin daukar Wilfried Zaha "ba irin wadanda yake so ba ne" kafin a rufe kasuwar sayen 'yan wasa.

Kazalika, Times ta ruwaito cewa Zaha ya shaida wa wakilansa cewa zai daina hulda da su bayan yunkurinsa na barin kungiyar Crystal Palace din ya ci tura.

A gefe guda kuma dai, Koci Hodgson ya ja kunnen magoya bayan Palace cewa "za a ci kwakwa" a sabuwar kakar da aka fara, in ji Standard.

Daraktan wasanni na Dortmund ya bayyana cewa kungiyarsa ta yi zaman tattaunawa da Manchester United kan dan wasan gaba Jadon Sancho, sai dai dan wasan ne bai nuna sha'awar komawa Old Trafford ba. (Mirror)

Manchester United za ta iya bai wa Solskjaer damar sayan dan wasan tsakiya a watan Janairu, yayin da jami'an kulab din suke kokarin fito da kudi domin karfafa kungiyar, in ji Manchester Evening News.

Labarai masu alaka