Na so Barcelona ta kara sayen Neymar - Messi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Neymar ya haskaka sosai a Barcelona tare da Messi da Suarez

Shahararren dan kwallo a duniya, Lionel Messi, ya ce ya so Neymar ya koma Barcelona da murza leda domin "taimaka wa kungiyar ta cimma burinta".

Neymar, dan shekaru 27, ya koma Paris St-Germain ne daga Barcelona a shekarar 2017 a matsayin dan kwallon da ya fi kowanne tsada a duniya kan kudi fan miliyan 200.

Messi ya shaida wa jaridar 'Sport' da ake wallafawa a harshen Spaniyanci cewa "Neymar ya zaku ya komo nan, amma ban sani ba ko kungiyar ta yi kokari a kai ko kuma a'a".

Neymar ya zura kwallo 105 a wasa 186 da ya buga a Barcelona tun daga shekarar 2013 zuwa 2017.

Sannan kuma a PSG ya ci kwallo 51 cikin wasa 58.

A kasuwar musayar 'yan kwallo, an yi ta alakanta Neymar da komawa Barcelona amma har aka rufe kasuwar musayar ba a cimma yarjejeniya a kan cinikinsa ba.