Ancelotti ya koka kan gyaran filin wasa na Napoli

Carlo Ancelotti Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ancelotti ya karbi Napoli a 2018

Kungiyar Napoli mai buga gasar Serie A ta kasar Italiya ta buga wasanninta biyu na farko ba a gida ba yayin da ake aikin gyaran filin wasa na San Paolo.

"Za ka iya gina gida cikin wata biyu amma sun kasa gama yi wa dakin shiryawar 'yan wasa kwaskwarima," in ji kocin Napoli Carlo Ancelotti.

Napoli za ta karbi bakuncin Sampdoria a ranar Asabar, kafin karawarsu da Liverpool a wasan farko na gasar Zakarun Turai ta Champions League a ranar Talata.

A wani bayani da aka wallafa a shafin kungiyar na intanet, Ancelotti ya ce: "Na ga yanayin da dakin shirin 'yan wasan yake ciki a San Paolo.

"Babu yadda na iya da bukatar kulab din ta cewa a buga wasanni biyun farko a wajen San Paolo domin a bai wa ma'aikata damar kammala aikin kamar yadda aka yi alkawari. Ya ya na iya!

"A ina 'yan wasanmu za su shiga su shirya a wasanmu da Liverpool da kuma Sampdoria? Ban ji dadin rashin kwarewar wadannan ma'aikata ba."

Jaridar La Gazzetta dello Sport ta ruwaito Filomena Smiraglia, wanda shi ne injiniyan da yake jagorantar aikin, yana cewa "na kadu da jin wadannan kalamai na Ancelotti".

"Mataimakin Shugaban Napoli Edoardo de Laurentiisya ya kawo mana ziyara kuma ya yaba mana kan aikin a gaban ma'aikata."

A ranar Alhamis Napoli ta wallafa wani bidiyo a Twitter mai dauke da hotunan halin da dakin shiryawar 'yan wasan yake ciki.

Labarai masu alaka