Solskjaer ya fahimce mu – Rashford

Marcus Rashford Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar Asabar ne kungiyar Maza ta karfi bakuncin kungiyar Leicester City

Dan wasan gaban Manchester United Marcus Rashford ya ce kocin kungiyar Ole Gunner Solskjaer ya fahimci 'yan wasan kungiyar.

Dan kwallon ya ce kasancewar Solskjaer tsohon dan wasa ne a kungiyar ta sa ya fahimci aikinsa na jagorancin kungiyar fiye da magabacinsa Jose Mourinho.

"A halin yanzu kowa yana da kwarin gwiwa. Ba lalle mu iya yin dukkan abin da ya bukaci mu yi ba, amma salon wasan yana kayatarwa. Dukkan 'yan wasa suna tare da shi," in ji Rashford.

Har ila yau ya ce Solskjaer yana da bambanci sosai da Mourinho.

A watan Disamban shekarar 2018 kungiyar Manchester United ta kori Mourinho, bayan ya shafe shekara biyu da rabi yana jagorantar kungiyar.

Mourinho mai shekara 55 ya lashe gasar League Cup da kuma Europa League a zamansa na Manchester United.

A yanzu dai United ita ce ta takwas a teburin gasar firimiyar Ingila.

A ranar Asabar ne kungiyar za ta karbi bakuncin kungiyar Leicester City a filin wasa na Old Trafford.

Labarai masu alaka