NFF za ta bayyana makomar Salisu Yusuf

Salisu Yusuf Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Salisu Yusuf shi ne mataimakin kochin Najeriya a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a 2018 da aka yi a Rasha

Kwamitin zartaswa a hukumar kwallon kafa ta Najeriya zai bayyana shawarwarin da aka yanke kan makomar Salisu Yusuf na cigaba da rike mukamin mataimakin mai horas da 'yan wasan kungiyar kwallon kafar kasar Super Eagles.

Wannan na zuwa ne bayan shekara guda dakatar shugaban kungiyar 'yan kasa da shekaru 23, sakamakon saba dokar hukumar.

An dakatar da Salisu Yusuf mai shekaru 57 ne tare da bashi tarar Dala 5000 a watan Satumbar bara, bayan da aka gano shi a wani faifan bidiyo yana karbar na goro a hannun wasu da suka yi badda kama suka fito a matsayin dillalan 'yan wasa.

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta tabbatar da cewa wa'adin dakatarwar da aka bai wa babban jami'in ya kare, kuma nan gaba kadan ne ake sa ran kwamitin zartaswar hukumar zai bayyana makomar sa.

"An dakatar da Salisu Yusuf ranar biyar ga watan satumbar 2018, sai dai a yanzu yana da damar sake komawa hukumar," kamar yadda Olajire ya shaidawa BBC.

"Bari na jaddada cewa har yanzu ba a mayar da Salisu Yusuf kan mukamin sa na mataimakin Gernot Rohr ba, kuma ba a mayar da shi kujerarsa ta shugabancin kungiyar 'yan kasa da shekara 23 ba." Inji Olajire.

Kwamitin zartaswar Hukumar Kwallon Kafar kasar NFF zai yanke hukunci game da komarwa sa bakin aiki.

"Mun fahimci cewa al'ummar kasar na jiran hukuncin da za a yanke, sai dai akwai bukatar a tattauna kan batun kafin sanar da hakan a kan lokacin da ya dace."

Olajire ya bayyana haka ne bayan sanarwar da Hukumar Kwallon Kafar Najeriya ta fitar game da karewar wa'adin dakatarwar da aka yiwa mataimakin Gernot rohr din.

Salisu Yusuf na daya daga cikin manyan masu horaswa da suka samu karbuwa a Yammacin Afirka, amma matsayin sa ya fuskanci wasu matsaloli sakamakon faifan bidiyon da aka nuna yana karbar na goron.

Kamar yadda rahotanni suka tabbatar an hasko shi a faifan bidiyon yana karbar tsabar kudi daga hannun wasu dillalan 'yan wasa da suka bukaci a sanya mutane biyu da zasu fafata a gasar cin kofin duniya.

Shi dai babban jami'in yana cigaba da musanta zarge-zargen da ake masa, kuma komawarsa kungiyar Super Eagles ya kawo rarrabuwar ra'ayi.

Yusuf ya kasance mataimakin kocin kungiyar Super Eagles Gernot Rohr a yayin gasar cin kofin duniya da aka gudanar a shekarar 2018 a kasar Rasha.

Labarai masu alaka