Neymar, Icardi, Messi, Sarri – muhimman abubuwa hudu da ke jan hankali a Turai

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lionel Messi ne ya ci kwallaye 36 daga cikin 90 da Barcelona ta zura a kakar wasan da ta wuce

A karshen mako za a koma tamaula a gasar kwallon kafa a Turai bayan dawowa daga hutu domin buga kwallo ta kasa da kasa.

Shin Neymar zai buga wasansa na farko a gasar bana a Paris St-Germain?

Ko Mauro Icardi ya soma nadamar komawa PSG daga Inter Milan ?

Karshen Lionel Messi ya kusa zuwa a Barcelona ?

Sashen wasanni na BBC ya yi nazari kan muhimman abubuwa na kwallon Turai.

Wacce irin tarba za a yi wa Neymar ?

Bayan ya buga wa Brazil kwallo a wannan makon, watakila a ranar Asabar Neymar ya murza leda a PSG a karon farko a kakar wasan bana.

Tambayar a nan ita ce: tun da ya yi kokarin ficewa daga kungiyar, shin wacce irin tarba dan wasan zai samu ?

Neymar mai shekaru 27, ya ji rauni a idon sawunsa a bazarar bana, kuma kawo yanzu bai buga kwallo a rigar PSG ba a kakar wasan bana.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Neymar ya kulla yarjejeniyar shekaru biyar tare da PSG a 2017

Bayan an yi ta alakanta shi da komawa Barcelona, magoya bayan PSG sun daga kyalle a filin wasa mai dauke da sakon 'Neymar ka tafi' a cikin watan Agusta.

"Shin zai buga wa PSG a ranar Asabar a wasansu da Strasbourg ? Kungiyar na bukatarsa," in ji masanin kwallon kafa Julien Laurens.

Guillem Balague, masanin kwallon Spaniya, ya ce ya dauka ungulu za ta koma gidanta na tsamiya, watau Neymar ya koma Barca.

'Ba da zuciya daya Icardi ya bar Inter ba'

Kamata ya yi lamarin ya zama sabon babi ga Icardi, lokacin da dan kwallon Argentina din ya koma PSG a matsayin aro daga Inter Milan a ranar 2 ga watan Satumba.

Amma rahotanni sun ce, matar dan kwallon mai shekara 26, watau Wanda Nara ta bayyana komawarsa kwallo a Faransa a matsayin mummunan zabi ga dan kwallon, saboda zai bar iyalansa a Italiya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Matar Icardi, Wanda Nara - ita ce wakiliyarsa

"Icardi ya so ya lallabi kocin Inter Antonio Conte, amma kuma abin bai yiwu ba," in ji kwararre James Horncastle.

'Shekaru biyu suka rage wa Messi a Barca ?'

Ko Messi na kan hanyarsa ta barin Barcelona ?

Bayan lashe kofuna gasar La Liga 10 da kuma na zakarun Turai hudu, dan wasan Argentina din zai iya wata sabuwar bajinta a Nou Camp kuwa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tun a ranar 25 ga watan Mayu rabon da Messi ya murza leda a Barcelona

A yanzu dan wasan yana fama da jinya, kuma ba zai kai shekara 40 yana murza leda," in ji Balague.

'Tsohuwar zuma'

Juventus ta lashe wasanni biyu a jere karkashin jagorancin Maurizio Sarri duk da cewa yana fama da ciwon sanyin hakarkari.

A ranar Asabar, kocin mai shekaru 60 wanda yake da jarabar shan sigari, zai bayyana a cikin fili a matsayin kocin Juve inda za su fafata da Fiorentina.

"Sarri yana da dabaru irin na tsaffin masu horasda kwallo," in ji Horncastle.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sarri ya kulla yarjejeniyar shekaru uku tare da Juventus a watan Yuni bayan ya bar Chelsea