Dan Samuel Eto’o na shirin soma murza leda a Kamaru

Samuel Eto'o Hakkin mallakar hoto No credit

Kamaru ta gayyaci dan Samuel Eto'o mai suna Etienne Eto'o Pineda cikin tawagar 'yan kwallonta ta 'yan kasa da shekaru 17, domin buga gasar kofin duniya a Brazil.

Dan shekaru 17, zai iya bugawa Spaniya - watau kasar da aka haife shi , amma sai ya ce kasar mahaifinsa Kamaru zai murza wa leda.

Ba ya cikin tawagar 'yan kwallon kasar da ta lashe gasar cin kofin Afrika ta 'yan kasa da shekaru 17 a farkon bana a Tanzania.

A yanzu dan kwallon shi ne kyaftin din tawagar kungiyar Mallorca ta 'yan kasa da shekary 17 - watau daya daga cikin kungiyoyin da mahaifinsa ya murza wa leda.

Samuel Eto'o, wanda ya yi ritaya daga kwallo a farkon wannan watan, ya buga wa Kamaru na tsawon shekaru.

A halin yanzu dai hukumar kwallon Kamaru na jiran izini daga wajen kungiyar Mallorca, kafin Etienne ya hadu da tawagar Kamaru a sansanin 'yan kwallonta a Yaounde.

Kamaru na rukunin E a gasar kofin duniya ta 'yan kasa da shekaru 17, inda za ta fafata da Argentina, Spain da kuma Tajikistan.

Labarai masu alaka