Pep Guardiola ya ce Laporte ba zai buga wa City wasa ba

Aymeric Laporte Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An fitar da Aymeric Laporte daga cikin fili a kan makara

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce dan wasan bayan kungiyar Aymeric Laporte zai tafi hutun jinya har zuwa watan Janairu ko Fabrairun badi.

Aymeric Laporte mai shekara 25, an masa aiki a kafarsa ta dama ne bayan da ya samu rauni a karawar da kungiyarsa ta yi nasara kan Brighton da 4-0 ranar 31 ga watan Agusta.

Dan wasan ya samu rauni a kokon gwiwarsa lokacin da suka yi taho mu gama da dan bayan Brighton Adam Webster.

Guardiola ya ce: "Ba wani dadewa zai yi ba. Wata biyar zuwa shida zai yi yana jinya, muna sa ran dawowarsa daga nan zuwa Janairu ko Fabrairun badi."

Dan wasan bayan ya buga wasanni 35 a kakar bara.

Tafiyar Aymeric Laporte jinyar ya sanya Manchester City ta samu gibi a bangaren 'yan wasan bayanta.

Sai dai hakan zai tilasta wa Nicolas Otamendi da John Stones su kara zage damtse a bangaren baya.

Manchester City za ta buga wasanta ne da Norwich City ranar Asabar. Amma Guardiolar ya ce kungiyar ta bai wa 'yan wasan bayanta horo na musamman.

Labarai masu alaka