FIFA ta umarci Iran ta bar mata shiga kallon wasanni

Gianni Infantino Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino yayin da yake kallon daya daga cikin wasan da aka bai wa mata damar halartar kallo a 2018

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Gianni Infantino ya ce ya kamata kasar Iran ta bai wa mata damar halartar filayen wasanni.

Tun daga lokacin da aka kafa gwamnatin juyin juya hali a shekarar 1979 kasar ta Iran ta hana mata halartar filayen wasanni a lokacin da maza ke wasa.

Sai dai Infantino ya ce yana fatan kasar za ta samar da wani sauyi kan wannan al'amari.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A watan gobe ne kasar Iran din za ta karbi bakuncin wasan cancantar shiga gasar cin kofin duniya da za ta kara da Cambodia.

"Burinmu a bayyana yake. Ya kamata Iran ta bawa mata dama su rika halartar kallon wasanni a filin wasa," in ji Infantino

"Yanzu lokaci ne da ya kamata a bullo da sauye-sauye kuma FIFA tana jiran sakamako mai faranta rai, kuma muna son ya fara aiki ne a wasan da Iran din za ta karbi bakuncinsa a watan Oktoba."

A farkon watan Satumbar 2019 ne wata mace mai suna Sahar Khodayari ta rasu bayan da ta cinnawa kanta wuta, sakamakon hana ta shiga gidan kallo da aka yi a kasar ta Iran din.

Matashiyar wadda aka yi wa lakabi da "Blue Girl" an cafke ta a watan Maris, lokacin da take kokarin shiga wani gidan kallo.

A gasar cin kofin nahiyar Asiya da aka fafata a watan Nuwambar bara, an bar mata magoya bayan kwallon kafa halartar gidajen kallo.

Amma a watan Yuni an hana mata halartar gidajen kallo a wasan sada zumuncin da Iran din ta yi da Syria a filin wasa na Azadi da ke babban birnin kasar Tehran.

A ranar 10 ga watan Oktoba ne Iran din za ta kara da Cambodia a wasan cancantar shiga gasar cin kofin duniya.

Labarai masu alaka