Iran: Mata 3,500 sun sayi tikitin kallon wasan kwallon kafa

Female Iranian football fans attend a screening of a 2018 World Cup match at the Azadi Stadium in Tehran Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mata masoya kwallon kafa 3,500 a kasar Iran sun sayi tikitin shiga kallon wasan neman cancantar shiga Kofin Duniya da kasar za ta yi da Cambodia a Tehran ranar Alhamis.

Haramun ne ga mata shiga filayen wasanni a Iran domin kallon wasannin maza tun bayan juyin juya halin Musulunci a shekarar 1979.

Wata mace Sahar Khodayari ta rasu a watan da ya gabata bayan ta cinna wa kanta wuta lokacin da take jiran yanke mata hukunci bisa laifin yunkurin shiga kallon wasa, inda ta badda kama a matsayin namiji.

Hukumar kwallon kafa ta Fifa ta ce jami'an Iran sun "tabbatar mata" cewa za a bar mata shiga kallon wasanni bayan rasuwarta.

Kamfanin dillancin labaran kasar mai suna Irna ya ce tikiti 3,500 ne aka sayar na bangaren zaman mata a katafaren filin wasa na Azadi Stadium mai cin 'yan kallo har 78,000.

Rahoton ya kara da cewa cikin 'yan mintuna aka sayar da tikitin a ranar Juma'a.

Fifa ta ce an shaida mata cewa za a sayar da tikiti 4,600 ga mata a rukunin farko, sai dai tana fatan a kara yawansa domin a bai wa matan da yawa dama.

Sannan ta ce za ta tura wakili kallon wasan domin sa-ido game da yunkurin.

Wata kungiya Open Stadiums, mai neman a bai wa mata damar kallon wasa a Iran, ta ce an fara sayar da tikitin ne ba tare da wata sanarwa ba daga hukumar kwallon kasar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu masu gangamin kira da a kawo karshen haramta wa mata shiga kallon wasanni kenan a gasar Kofin Duniya da ta gabata

Saboda haka mata masoya kwallon kafa sai a shafukan sada zumunta suka samu labari.

An taba dage haramcin na dan wani lokaci a shekarar bara domin ba su damar kallon wasannin Kofin Duniya da aka haska kai-tsye a Azadi Stadium.

Kazalika, an bar wasu mata kalilan shiga kallon wasan karshe zagaye na biyu na gasar Asian Champions League a Tehran a watan Nuwamba.

Sai dai ba a bari sun kalli wasan sada zumunta ba tsakanin kasarsu da Syria a filin wasan na Azadi Stadium.

Labarai masu alaka