Tomori ya zabi Ingila maimakon yi wa Najeriya kwallo

Fikayo Tomori Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasan Chelsea, Fikayo Tomori ya ce ya zabi ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Ingila tamaula maimakon ta Najeriya.

Tomori mai shekara 21, wanda aka haifa a Canada wadda ya buga wa tawagar matasanta 'yan shekara 20 kwallo yana kuma da damar yi wa Najeriya tamaula.

Ya ce ''bai yi ''tsammanin'' Ingila za ta gayyace shi karawar da za ta yi da Jamhuriyar Czech da ta Bulgariya a wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Turai ba.''

Dan wasan ya ce duk ta inda ka hanga yana da damar zabin kasa daya daga ukun da ta cancanci ya buga wa kwallon kafa ya kuma amince ya sa rigar Ingila.

Yanayin Tomori iri daya ne da na Tammy Abraham wanda shima ke taka leda a Chelsea, wanda zai iya yi wa Najeriya wasa, amma Ingila ta gayyace shi tawagar kwallon kafarta.

Tun kan kocin Ingila Gareth Southagate ya mika masa goron gayyata, Abraham ya ce bai yanke hukuncin kasar da ya kamata ya buga wa tamaula ba.

Labarai masu alaka