Messi ya ce ya yi yunkurin barin Barcelona

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Getty Images

Lionel Messi ya ce ya so ya bar Barcelona a 2013, amma yanzu ya yanke hukuncin cewar a kungiyar zai yi ritaya daga taka leda.

Kyaftin din Argentina, ya fada a wata hira da wani gidan radiyo a Barcelona RAC 1 ya yi da shi, inda ya ce ''ba a kyauta min ba da aka tuhume ni da laifin kin biyan haraji.

Mahukuntan Spaniya ce suka tuhumi Messi da mahaifinsa da laifin cewar sun yi kokarin kin biyan haraji.

Messi ya ce ''Barcelona ba su yi min laifi ba, amma a lokacin ji na yi gwara na bar Spaniya da taka leda.

Ya kuma kara da cewar ''a lokacin kungiyoyi da dama sun yi zawarci na, amma an kasa cimma yarjejeniya ne saboda kowa ya san cewar bana son barin Barcelona.''

Messi ya koma Barcelona makarantar rainon 'yan kwallo La Masia tun yana da shekara 13, ya kuma fara buga wa babbar kungiyar wasa yana da shekara 16.

Daga nan ne kawo yanzu ya zama dan wasan da ya fi ci wa Barcelona kwallo a raga, yana da 604 kuma shi ne na biyu a yawan buga wa kungiyar wasanni bayan Xavi.

Messi ya kara da cewar ''babu wata sabuwar yarjejeniya da ya yi a Camp Nou, bayan wadda za ta kare a 2021, amma a Barcelona zan kammala wasannin tamaula.''

Kyaftin din Barcelona ya ce ''yana kyaunar kungiyar, kuma iyalansa suna jin dadin zama a Spaniya, saboda haka zai ci gaba da zamansa.''

Labarai masu alaka