Brazil za ta kara da Senegal da kuma Najeriya

Brazil Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mataimakin kocin tawagar kwallon kafar Brazil, Cleber Xavier na shirin fuskantar kalubale a wajen Senegal a wasan sada zumunta da za su kara a karon farko.

Haka kuma Brazil za ta fafata da tawagar Najeriya a jerin wasannin sada zumunta da za ta buga da tawagogin Afirka a Singapore.

Xavier ya shaidawa BBC cewar ''Tawagar Senegal tana da kwarewa, sannan tana da fitattun 'yan kwallo.''

''Ba a ci su kwallaye da yawa a gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka yi a Masar da suka kai karawar karshe ba, suna da kwararrun 'yan wasa kamar Sadio Mane da Idrissa Gueye.''

Wannan ne karo na biyu da Brazil za ta fafata da Super Eagles, bayan 2003 da ta yi nasara da ci 3-0 a karawar da suka yi a Abuja.

Wadanda suka ci wa tawagar kwallon kafar Brazil kwallayen sun hada da Gil da Luis Fabiano da kuma Adriano Leite.

Tawagar kwallon kafa ta Kamaru ce kadai daga Afirka ta taba doke Brazil 1-0 a Cnfederation Cup a shekarar 2003.

Brazil za ta buga wasan sada zumunta da Senegal ranar 10 ga watan Oktoba, sannan ta kara da Super Eagles ranar 13 ga watan Oktoban.

Labarai masu alaka