Ibrahimovic ya kaddamar da butun butuminsa

Ibrahimovic

Zlatan Ibrahimovic ya kaddamar da butun butuminsa a kusa da filin wasa da ya fara kwallo a matsayin kwararre a garinsa a Malmo.

An dau shekara biyar kan a kammala sassaka butun butumin, wanda gwanin sassaka dan kasar Sweden, Peter Linde ya yi aikin.

Ibrahimovic yana da tsawon kafa shida da inci biyar, inda aka sassaka butun butumin nasa na tagulla tsawon mita 2.7 mai kuma nauyin kilogram 500.

Ibrahimovic wanda ya taka leda a Paris St Germain yana da butun butuminsa da aka sassaka a dakin ajiye kayayyakin tarihi a Faransa.

Dan wasan wanda iyayensa 'yan kasar Yugoslavia ne ya yi rayuwarsa a matsanancin hali a Rosengard, unguwar da ke Malmo da ta yi kaurin suna wajen fada tsakanin 'yan daba da ke hamayya da juna.

Ibrahimovic ya buga wa Malmo kwallon kafa sai ya koma Ajax da Juventus da Inter Milan da Barcelona da AC Milan da PSG sai Manchester United daga nan ya koma LA Galaxy ta Amurka.

Dan wasan ya lashe kofi 13 a kakar tamaula 16 da ya yi a Netherlands da Italiya da Spaniya da Faransa, koda yake an karbe kofin da Juventus ta lashe a lokacinsa.

Kungiyarsa ta Galaxy ta kai wasan cike gurbi a gasar kwallon kafar Amurka, za kuma ta fafata da Minnesota a wasan farko ranar 20 ga watan Oktoba.

Ibrahimovic ya buga wa tawagar kwallon kafar Sweden kwallo sau 116 tsakanin 2001 zuwa 2016 wadda ya ci wa kwallaye 62.