Gareth Bale yana 'fushi da Real Madrid, yana so ya bar su'

Gareth Bale Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gareth Bale ya taimaka wa Real Madrid wajen cin kofin Zakarun Turai sau hudu a kakar wasa shida aka ya fafata tun da ya koma kulob din daga Tottenham a 2013

Dan jaridar BBC Radio 5 Live, Guillem Balague, ya yi ikirarin cewa dan wasan gaba na Real Madrid Gareth Bale ya "fusata sosai" da kulob din kuma yana matukar son barinsu.

An yi tsammani Bale zai sanya hannu kan kwantaragin shekara uku da kulob din Jiangsu Suning da ke buga gasar lig-lig a China a bazara - inda za a biya shi £1m a kowane mako - amma Real sun ki amincewa da hakan domin suna so a ba su kudin barin kulob, wato transfer fee.

A watan Yuli, kocin Real Zinedine Zidane ya ce "muna fata zai bar kulob din nan ba da dadewa ba", abin da ya sa wakilin Bale, Jonathan Barnett ya mayar da martani cewa: "Zidane abin kunya ne - ba ya martaba dan wasan wanda ya yi aiki tukuru a Real Madrid."

Bale ya lashe kofin Zakarun Turai hudu da na La Liga daya da Copa del Rey da na Uefa uku da kuma gasar cin kofin duniya ta kulob-kulob a Real, inda ya zura kwallo fiye da 100.

Bayan an hana shi komawa China, dan wasan mai shekara 30 dan kasar Wales, ya janye daga buga wasan sada zumunci na share-fagen kakar wasa ta bana a Munich - kuma an fahimci cewa ya dauki matakin ne saboda bai ji dadin abubuwan da ke faruwa da shi ba.

Ya koma Real a kakar wasan da muke ciki, ya zura kwallo biyu a wasa bakwai da ya shiga inda suka zama na farko a saman teburin gasar La Liga.

Sai dai ba a sanya shi a tawagar da ta buga wasan da suka yi da Club Bruges a gasar cin kofin Zakarun Turai ba.

"Gareth Bale ya gaji da zama a Real," in ji Balague. "Ba zai iya ci gaba da zama a kulob din ba. A daidai lokacin da ya soma tagazawa, inda yake ganin yana buga wasa domin maido da kuzarinsa, sai kawai aka ki sanya shi a karawar da aka yi da Bruges inda ya zama dan kallo. Babu wanda ya san dalilin yin hakan.

"Yana cike da fushi, ya rude. Lokacin da Zidane ya koma kulob din ya yanke shawarar mayar da Bale saniyar-ware, ba tare da wani dalili ba."

Labarai masu alaka