AC Milan: Pioli ne ya gaji Giampaolo a matsayin kocinta

Stefano Pioli Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Stefano Pioli ya ajiye aikinsa a Fiorentina a watan Afrilu

AC Milan ta nada Stefano Pioli a matsayin sabon kocinta biyo bayan sallamar Marco Giampaolo da ta yi a ranar Talata bayan wata uku da rabi kacal da ya jagoranci kungiyar.

Dan kasar Italiya mai shekara 53, Pioli shi ne tabbataccen koci na tara da Milan ta yi tun bayan da ta lashe gasar Serie A a shekarar 2011.

Maudu'in #PioliOut (ba ma son Pioli) shi ne wanda aka tattaunawa a shafin Twitter na kasar Italiya a ranar Talata, inda magoya bayan suka rika nuna rashin amincewarsu da nadin Pioli.

Milan dai tana mataki na 13 ne a teburin Serie A, maki uku kacal tsakaninta da 'yan kasan teburi.

Ta ci Genoa 2-1 ranar Asabar bayan golanta Pepe Reina ya bige finareti a mintunan karshe, abin da ya ba ta nasara a karo na uku kacal cikin wasa bakwai na gasar bana.

Kafin haka ta yi rashin nasara har sau uku a jere a hannun Inter Milan da Torino da Fiorentina.

Giampaolo mai shekara 52, ya gaji Gennaro Gattuso a watan Yuni bayan ya ajiye aikinsa saboda gaza samun gurbin shiga gasar Champions League.

Pioli ya bar kungiyar Sampdoria ne a karshen kakar da ta gabata bayan ya taimaka mata karewa a mataki na tara a Serie A.

Tshon kocin Inter Milan da Fiorentina da Lazio, Pioli ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyu a San Siro.

Rabon da AC Milan ta buga gasar Zakarun Turai ta Champions League tun a 2013-2014 - ta lashe gasar sau bakwai a tarihi.

Ya kamata a ce kungiyar tana buga gasar Europa amma tana kammala hukuncin dakatarwa na shekara daya da hukumar kwallon kafar Turai ta Uefa ta yi mata game da saba dokar kashe kudi.

Labarai masu alaka