Man Utd na zawarcin Rice, Guardiola 'zai ajiye mukaminsa'

Pep Guardiola Hakkin mallakar hoto Reuters

Manchester United na duba yiwuwar sayo dan wasan tsakiya na West Ham da Ingila Declan Rice, mai shekara 20, da kuma dan wasan Napoli da Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 28, ba tare da la'akari da makomar kocinsu Ole Gunnar Solskjaer ba. (Goal)

Manchester United za su bai wa kocinsu Solskjaer karin lokaci domin ya inganta yadda kulob din yake murza leda, duk kuwa da cewa wannan ne karon farko da suka soma kakar wasa da kafar hagu a cikin shekara 30. (Telegraph)

Sai dai, a cewar wani rahoto, hukumar gudanarwar kulob din ta ce za ta sallame shi idan Manchester United ta sha kashi a hannun Norwich a wasan da za su buga a karshen wata. (Sun)

Manchester United na son daukar matashin kocin RB Leipzig dan kasar Jamus Julian Nagelsmann, mai shekara 32, domin zama sabon kocinsu. (Mail)

Kocin Tottenham Mauricio Pochettino na shirin sayar da dan wasan Ingila na tsakiya Eric Dier, mai shekara 25, da dan kasar Denmark mai shekara 27 Christian Eriksen, da dan kasar Ivory Coast Serge Aurier, mai shekara 26, da dan kasar Kenya Victor Wanyama, mai shekara 28, da kuma dan kasar Ingila mai shekara 29 Danny Rose a watan Janairu bayan da suka gaza yin katabus a farkon kakar wasa ta bana. (Times - subscription required)

Jose Mourinho yana sanya ido a kan abubuwan da ke faruwa a Tottenham a yayin da yake tunanin sake komawa fagen horaswa bayan an sallame shi daga Manchester United a 2019. (Mail)

Dan wasan Tottenham da Ingila Dele Alli, mai shekara 23, ya dauki hayar masani kan abinci a wani mataki na hana samun rauni a jijiyoyinsa bayan ya ji rauni sau hudu a cinyarsa cikin wata 18 da suka gabata. (Mirror)

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce 'zai koma gefe guda' idan har al'amura basu tafi yadda yake so ba bayan Liverpool sun bai wa City tazarar maki takwas a gasar Firimiya. (Sun)

A shirye David Moyes yake ya koma tsohon kulob dinsa Everton, bayan da kocin kulob din Marco Silva ya ci gaba da fuskantar matsin-lamba saboda sun fada matakin fita daga gasar Firimiya. (Mirror)

Crystal Palace za su biya £22m domin sayen dan wasan Chelsea dan kasar Belgium mai shekara 26 Michy Batshuayi, wanda ya kwashe rabin kakar wasan da ta wuce a Selhurst Park a matsayin aro. (Express)

Dan wasan tsakiya na Arsenal Dani Ceballos, mai shekara 23, ya ce ya dauki matakin da ya dace wajen komawa kulob din a matsayin aro daga Real Madrid bayan da ya koma matsayinsa a Madrid din. (Goal)

Tsohon dan wasan gaba na Sunderland Kevin Phillips yana son zama kocin kulob din bayan korar kocinsu Jack Ross. (Star)

Sai dai watakila tsohon kocin Barnsley Daniel Stendel zai iya maye gurbin Ross. (Sun)

Borussia Dortmund sun bi sahun Arsenal, Juventus da kuma Paris St-Germain wajen bibiyar dan wasan Celtic Karamoko Dembele, mai shekara 16. (Bild - in German)

Labarai masu alaka