Neymar zai yi wa Brazil wasa na 100

Neymar Hakkin mallakar hoto Getty Images

Neymar zai buga wa tawagar kwallon kafa ta Brazil kwallo na 100 a wasan sada zumunta da za ta yi da Senegal.

Tuni kocin Brazil ya bayyana 'yan wasan da za su buga masa karawar a Singapore, ciki har da mai tsaron ragar Manchester City, Ederson da dan kwallon Liverpool, Roberto Firmino.

Neymar ya ci wa tawagar Brazil kwallo 61 a wasa 99 da ya yi mata kawo yanzu, saura daya ya yi kan-kan-kan da Ronaldo, saura 16 ya kamo Pele.

Brazil wadda ta lashe Copa America za ta kara da Senegal a wasan sada zumunta a karon farko, wadda ta kai wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar Afika da aka yi a Masar.

Brazil din za ta fara yin wasan sada zumunta da Senegal ranar 10 ga watan Oktoba, sannan ta kara da tawagar kwallon kafar Najeriya kwanaki uku tsakani a Singapore.

Wannan ne karo na biyu da Brazil za ta fafata da Super Eagles tun 2003 lokacin da ta yi nasara da ci 3-0 a Abuja.

Mataimakin kocin Brazil, Cleber Xavier ya shaidawa BBC cewar wasannin sada zumuntar da za su yi zai taimaka musu gwada matasan 'yan wasansu da wasu sabbi da suka gayyata.

Ya kara da cewar sun yi irin haka kan gasar Copa America shi ya sa suka samu damar lashe kofin ganin shiri da suka yi tun da wuri.