Man U na son sayen 'yan wasa shida, Zidane na son Pogba

Pogba Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kocin Everton Marco Silva na da wasanni uku kacal da kungiyar tasa za ta taka domin fitar da ita kunyar da ta kwasa a farkon wanninta na kakar nan kasancewar yanzu kulob din na daga cikin guda uku da ke karkashin teburin gasar Premier.

Manchester United ta shirya tsaf domin biyan fan 130m domin sayen 'yan wasan Leicester City, James Maddison da Ben Chilwell dukkannin su masu shekara 22. (Sun)

To sai dai akwai yiwuwar Ben Chilwell zai tafi Chelsea ne da zarar an dage musu haramcin matsawa daga wani kulob zuwa wani. (Mail)

Manchester United na son sayen 'yan wasa takwas a kakar musayar 'yan wasa guda biyu masu zuwa kuma tuni ta fitar da jerin sunayen 'yan wasan da take hako. (Telegraph)

Juventus za ta bayar da dan wasanta dan asalin kasar Mario Mandzukic, mai shekaru 33 tare da Emre Can mai shekara 25 domin a ba ta dan wasan Manchester United na tsakiya, Paul Pogba mai shekar 26. (Sun)

ottenham Hotspur na fatan sayar da dan wasanta mai shekara 27 wato Eriksen a watan Janairu domin yin rigakafi daga rasa dan wasan a lokacin da kwantaraginsa ya kare a lokacin bazara mai kamawa. (Mirror)

To sai dai duk yadda hankalin shugaban Real Madrid, Florentino Perez ya fi karkata ga Eriksen, amma kocin kungiyar Zinedine Zidane ya fi son dan wasan Manchester United, Pogba mai shekara 26. (ESPN)

Kocin Juventus, Maurizio Sarri na son sayen dan wasan Chelsea , Emerson Palmieri, mai shekara 25. (Express)

Arsenal na tattaunawa da Fenerbahce na Turkiyya kan Mesut Ozil mai shekara 30. (Takvim - in Turkish)

Manchester City na duba yiwuwar sayen dan wasan Benfica dan asalin kasar Portugal mai shekara 22, Ruben Dias wanda ake raderadin ita ma Manchester United na zawarci. (Mirror)